Hausa Proverbs

1) Karin Magana
Anyi ba ayi ba, rufe ƙofa da ɓarawo.

Ma'ana
Abinda ake kaucewa ne ya kasance ana tare dashi cikin rashin sani.
2) Karin Magana
Ba ayi ciki don tuwo ba kawai ba.

Ma'ana
Kowa yanada nasa sirrin wanda ba kowa ya sani ba.
3) Karin Magana
Ba da ni ba, gaɗa a hurumi.

Ma'ana
Gujewa aikata aikin da zai jawo matsala a gaba.
4) Karin Magana
Ba girin-girin ba, ta yi mai.

Ma'ana
Ba ɗokin aikata wani abu ba ya kasance a ƙarshen sa akwai alfanu aciki.
5) Karin Magana
Ciki da gaskiya, wuƙa bata huda shi.

Ma'ana
Matuƙar mutum ya rike gaskiya, to ba zai kunyata ba.
6) Karin Magana
Da rarrafe yaro ya kan tashi.

Ma'ana
Duk abinda ka sa a gabanka wata rana za ka kai ga ci.
7) Karin Magana
Da walakin, goro a miya.

Ma'ana
Duk inda ka ga wani abu, to akwai dalilinsa.
8) Karin Magana
Dare mahutar bawa.

Ma'ana
Komai da lokacinsa.
9) Karin Magana
Duk girman ɗantsako, ƙwai ya fi shi.

Ma'ana
Duk daraja da girman mutum asalinsa ya fishi.
10) Karin Magana
Duk wanda ya daka rawar wani, zai rasa turmin daka tasa.

Ma'ana
Duk wanda ya biyewa san ran wani, to zai ƙare a wahala.

MOBILE APP COMING SOON ON